January 15, 2025

Barcelona za ta yi bincike kan cin zarafin da magoya bayanta suka yi wa Vinicius

1
33ZA7D8-Preview-1024x684.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Barcelona ta ce za ta binciki zargin cin zarafin da aka yi wa Vinicius Junior a wasan ElClasico da Real Madrid ta doke su da ci 2-1 ranar Asabar.

Wani faifan bidiyo da kafafen yada labarai na Sifaniya suka buga ya nuna wani mai goyon bayan gida yana kiran dan wasan na Brazil da “biri”, yayin da wani abu mai kama da fatar ayaba shima ya bayyana daga wani waje.

“FC Barcelona za ta ci gaba da kare martabar ƙwallon ƙafa da wasanni wand aya haɗa da mutunta abokin hamayya kuma za mu binciki duk wani cin mutuncin wariyar launin fata da ya faru da yammacin yau yayin wasa da Real Madrid,” in ji Barcelona.

Vinicius, wanda magoya bayan Barca suka yi masa ihu a filin wasa na Olympics na Barcelona musamman ya ba shi haushi lokacin da aka sauya shi da wuri bayan Jude Bellingham ya ci kwallonsa ta biyu.

Tun ba yau na Vinicius yake fuskantar irin wannan cim zarafi a fagen wasan Sifaniya.

1 thought on “Barcelona za ta yi bincike kan cin zarafin da magoya bayanta suka yi wa Vinicius

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *