Bankin Duniya zai ba da tallafin dala miliyan 20 a Gaza

Daga Sabiu Abdullahi
Bankin Duniya ya sanar cewa zai ba da sabon tallafin da ya kai dala miliyan 20 don samar da taimakon jinƙai ga mutanen Gaza.
Wani rahoto da TRT Hausa ta fitar ya nuna cewa bankin zai kuma haɗa da dala miliyan 10 don sayen kayan abinci.
Rahoton ya ce, “Sanarwar da bankin ya fitar ta ce, tallafin zai kai ga kimanin mutum 377,000, wani ɓangare ne na wani babban shirin agaji na dalar Amurka miliyan 35 ga Zirin Gaza.”
A halin yanzu dai an riga an kai dala miliyan 15 na farko domin samar da agajin gaggawar.