Bankin Duniya Ya Yi Hasashen Karuwar Talauci a Najeriya Nan da Shekarar 2027

Bankin Duniya ya bayyana cewa ana sa ran talauci zai karu da kaso 3.6 cikin dari a Najeriya nan da shekarar 2027.
Wannan hasashe na kunshe ne a cikin rahoton Africa’s Pulse da aka fitar yayin taron bazara da ake gudanarwa tsakanin Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a birnin Washington, D.C.Rahoton ya nuna fargaba dangane da kokarin rage talauci a Najeriya.
Duk da wasu ci gaba da aka samu a bangaren tattalin arziki, musamman a sashen da ba na mai ba a karshen shekarar 2024, Bankin Duniya ya bayyana cewa matsalolin tsarin tattalin arziki da dogaro da albarkatu da kuma rashin daidaiton siyasa za su ci gaba da zama kalubale.
Bankin ya bayyana cewa Najeriya da sauran kasashe masu albarkatu da fama da rikice-rikice a yankin Kudu da Saharar Afirka za su fuskanci karuwar talauci, sabanin kasashen da ba su dogara da albarkatun ba.
Rahoton ya kuma nuna cewa yankin Kudu da Saharar Afirka ne ke da mafi yawan talakawa a duniya.
A shekarar 2024, kashi 80 cikin dari na mutanen duniya miliyan 695 da ke fama da talauci matuƙa suna zaune ne a wannan yanki. Rabin mutane miliyan 560 da ke cikin talauci a yankin suna zaune a ƙasashe guda huɗu kacal.
A bangaren sauran yankuna, Kudancin Asiya na da kaso 8 cikin dari na talakawan duniya, Gabashin Asiya da Tekun Pasifik 2 cikin dari, Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka 5 cikin dari, sai Latin Amurka da yankin Caribbean da ke da 3 cikin dari.