Babu wanda zai iya hana ni neman a saki Nnamdi Kanu – Aguocha
Daga Ɗanlami Malanta
Mamba mai wakiltar mazaɓar Ikwuano/Umuahia Ta Arewa/Umuahia Ta Kudu, Hon. Obi Aguocha, ya yi alkawarin bijire wa duk wata barazana a yunƙurinsa na fafutukar ganin an sakin Mazi Nnamdi Kanu.
Aguocha ya jaddada cewa ba za a hana shi ko tursasa shi ba a yunkurinsa na ganin an sako shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu daga tsare shi ba bisa ka’ida ba.
Da yake jawabi a babban taron makon ‘yan jarida na 2023 na Ƙungiyar aƳan Jarida ta Najeriya (NUJ), da aka gudanar a cibiyar taro ta Aguiyironsi da ke Umuahia, Aguocha ya tabbatar da cewa Kanu shi ne wanda ya fito da shi kai tsaye.
Ya kuma jaddada cewa sakin Kanu zai taimaka wajen zakulo masu fakewa da sunan fafutukar kafa kasar Biafra wajen aikata miyagun laifuka a yankin Kudu maso Gabas.
Ya ce: “Ya kamata a sako Kanu domin zaman lafiya ya dawo a kudu maso gabas. Halin rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas yana da ban tsoro, kuma kowa ya yi ta nuni da ci gaba da tsare Kanu. me zai hana a sake shi bisa ga umarnin kotu? Idan aka sake shi, za mu san wadanda suke fakewa da su domin tayar da tarzoma a kasarmu”.
Dan majalisar ya bukaci ‘yan jarida da su nuna jajircewa wajen fadin gaskiya ga masu mulki ba tare da tsoro ba, ba tare da la’akari da illar da hakan zai iya haifarwa ba.
Ya ce, “Ya kamata ‘yan jarida su ci gaba da tofa albarkacin bakinsu; kada su ji tsoro”.
Ya bayyana manema labarai a matsayin muhimmin ginshikin dimokuradiyya sannan ya yi kira da su rika bayar da rahotanni na gaskiya da gaskiya
наркологическая скорая бесплатная наркологическая скорая бесплатная .
нарколог на дом вывод из запоя на дому нарколог на дом вывод из запоя на дому .
Лечение химической зависимости в Казахстане Лечение химической зависимости в Казахстане .
официальный курс доллара официальный курс доллара .
вип проститутки https://drive-models.ru .
стационарное лечение алкоголизма стационарное лечение алкоголизма .
instagram viewer private instagram viewer private .