Babu Alaƙa Tsakanin Maulidi da Qur’anic Convention – Dr. Jalo Jalingo

Shahararren malamin Izala Najeriya, Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, ya bayyana cewa babu wata alaka ko kusanci tsakanin Mauludin Annabi (Maulid) da Qur’anic Convention da kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a wa Iqamatus Sunnah ta shirya kwanan nan.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dr. Jalo Jalingo ya bayyana cewa Qur’anic Convention taro ne da ake yi domin karatun Alƙur’ani mai girma da fahimtar fannoninsa, wanda Annabi Muhammad (SAW) ya umarci al’ummar Musulmi da su yi.
Ya ce akwai nassoshi da dama daga hadisan Annabi (SAW) da ke kwadaitar da irin wannan taro, kuma nan gaba za su kawo wasu daga cikinsu domin fadakar da al’umma.
Dangane da Maulidi, malamin ya jaddada cewa, “Shi kuwa idin Maulidi kirkirar wata ibadah ce da babu umurnin Annabi game da ita laa min qareebin walaa min ba’eed. Sam sam sam Annabi mai tsira da amincin Allah bai kwadaitar da cewa al’ummar Musulmi su yi taron Maulidi ba.”
A cewarsa, babu wani hadisi da ya ambaci bukin Maulidi ko ya kwadaitar da shi, don haka ya zama kirkirarren abu da bai da tushe a addini.
Dr. Jalo Jalingo ya kara da cewa wasu mutane na kokarin nuna Qur’anic Convention ta hanyar hada shi da Maulidi, amma wannan abu ne da ya samo asali daga son zuciya da shirin tayar da hayaniya a cikin al’umma.
Ya ce Qur’anic Convention yana da ingantaccen tushe daga shari’a saboda ana gudanar da shi ne domin karatun Alƙur’ani da fahimtar ma’anarsa, yayin da Maulidi kirkirarren abu ne da aka ƙirƙira kuma ake yi a duk shekara da sunan neman lada.
A ƙarshe, malamin ya bukaci Musulmi da su nisanci duk wani abu da bai da asali a addini, su kuma rungumi yin taruka na karatun Alƙur’ani da koyon addini kamar yadda Annabi (SAW) ya umarta.
Wannan na zuwa ne bayan taron an Qur’anic Convention ya sha suka daga wani bangare na al’ummar Muslunci.
suhwu5