Babu abinda ƙarin kuɗin fetur zai kawo wa Nijeriya sai ci gaba—Tinubu

Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu abin da ƙarin kuɗin man fetur zai yi sai taimaka wa Nijeriya wajen samun ci gaba ta fuskar tattalin arziki.
Tinubu ya faɗi haka ne a ƙasar China lokacin da yake ganawa da ‘yan Nijeriya mazauna can a jiya Juma’a.
A cewar shugaban, kamar yadda wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar ta bayyana, “Najeriya na fuskantar sauye-sauye, kuma muna ɗaukar muhimman matakan da suka dace.”
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa samar da kayan more rayuwa kyauta ko cikin farashi mai sauƙi babu abin da zai yi sai ƙara jefa ‘yan ƙasa cikin wahala.
Tinubu ya ce jazaman ne gwamanati ta ɗauki muhimman matakai in har ana buƙatar Najeriya ta bunƙasa.
Ya kuma bayyana cewa samar da kayan more rayuwa kyauta ko cikin farashi mai sauƙi babu abin da zai yi sai ƙara jefa ‘yan ƙasa cikin wahala.
“Daga lokacin da kuke son samun abu kyauta, to a lokacin ne abubuwan za su ƙara tsada, sannan a samu jinkiri wajen samun ci gaba mai ma’ana,” a cewarsa.
Taron da Tinubu ya yi da ‘yan Najeriya a China shi ne abu na ƙarshe da ya yi a ziyarar da ya kai don taron China da shugabannin Afirka , kafin tafiyarsa Dubai.
Daga nan kuma kuma zai wuce zuwa Birtaniya.