Babban layin wautar lantarki na ƙasa ya sake lalacewa
Daga Abdullahi I. Adam
Babban layin wautar lantarki na ƙasa ya sake lalacewa cikin daren da ya gabata kamar yadda bayanai ke nunawa.
Layin wutar, wanda kan iya samar da wuta mai ƙarfin mega wat 2,583.77 a wajajen ƙarfe biyu na daren jiyan, sai da ya dawo ƙasa zuwa bada wuta mai ƙarfin mega wat 64.7 kacal.
Kamar yadda hukumar wuta ta ƙasar ke iƙirari, lalcewan babban layin wutar kan auku ne saboda ƙarancin iskar gas, ayyukan masu fasa bututun mai da dai sauransu.
A bayanan da ya fitar, wani babban jami’i na hukumar a shiyyar Jos, Dr. Friday Elijah, ya ce rashin wutar da ake fama da shi ya faru ne saboda rasa wutar da aka yi a babban layin wutar na ƙasa kwata-kwata.
Haka zalika jami’in ya ba abokan hulɗar kamfanin haƙuri da yi masu albishir cewa wutar za ta samu ba da jimawa ba.