May 13, 2025

Babban jami’in Hizbullah Safa Yahaya ya sha da ƙyar bayan harin da Isra’ila ta kai Beirut

FB_IMG_1728641825674.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Dakarun Isra’ila sun kaddamar da hare-haren sama da suka nufaci Wafiq Safa, babban jami’in Hizbullahi. 

Safa, wanda shi ne shugaban Sashen Hulda da Tsare-tsare na kungiyar, ya tsira daga yunkurin kisan. 

A cewar jaridar Economic Times, duk da haka, harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 22 tare da jikkata fiye da 100 a unguwannin tsakiyar Beirut. 

Hare-haren sun shafi yankunan da suka hada da Al Nuwairi, Ras el-Nabaa, da unguwar Basta.

Hukumar lafiya ta Lebanon ta bayyana cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa saboda mummunar lalacewar gine-gine da kayayyakin more rayuwa a wuraren da suka yi cunkoso sosai. 

Shaidu sun bayyana yanayi mai cike da rudani, inda motocin daukar marasa lafiya ke fama wajen isa wuraren da suka fi tsananta, yayin da wasu gidaje suka cika da duwatsu. 

Idan ba a manta ba, Wafiq Safa ya taka muhimmiyar rawa a tattaunawar yankin, ciki har da taimakawa wajen musayar fursunoni tsakanin Hizbullahi da Isra’ila a shekarar 2008.