January 15, 2025

Babban Bankin Najeriya ya soke lasisin Bankin Heritage

0
Heritage-Bank-e1716237695940.jpg

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da cewa ya soke lasisin bankin Heritage.

Cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne “domin tabbatar da ingantaccen tsarin kudi a ƙasar, kuma ya yi hakan ne a karkashin sashe na 12 na dokar bankuna da sauran harkokin kudi (BOFIA) ta 2020”.

A cewar bankin, soke lasisin ya zama dole ne bayan da bankin na Heritage ya ci gaba da saba wa sashe na 12 (1) na BOFIA 2020 da gazawarsa wajen inganta ayyukansa na kuɗi inda yake haifar da babbar barazana ga daidaiton kuɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *