January 14, 2025

Babban Ɗan Ƙwallon Da Bai Taɓa Samun Katin Gargaɗi Ko Jan Kati Ba

0
IMG-20240123-WA0003.jpg

Daga Katib AbdulHayyi

Shin ba zai ba ka mamaki ba idan aka ce ga wani ɗan ƙwallon da ya taka leda na tsawon shekaru 16 a gasar Firimiyar Ingila da La Liga a Sifaniya ba tare da samun ko da katin gargaɗi (yellow card) ba?

Idan ana maganar wannan ɗan wasa masanin zura ƙwallaye da ya kafa tarihin zama kan gaba wajen zura ƙwallaye a lokuta daban-daban, har a kulob uku, ba maganar jan kati ake ko katin gargaɗi ba. Ko harara ba ta shiga tsakaninsa da abokan wasa.

Tsakanin shekarar 1978 zuwa 1994, Gary Lineker, tsohon ɗan wasan Ingila da Barcelona ya bayyana cikin tarihi daban-daban na ƙwallon ƙafa, kama daga rashin samun kati ko sau ɗaya duk da shafae shekaru 16 yana murza zarensa, cin kyautar mafi cin ƙwallaye a gasa daban-daban da kulob uku na Ingila.

Kamar yadda Christiano Ronaldo ya kafa tarihin zama mafi cin ƙwallaye a gasa daban-daban na duniya, Lineker kuma ya kafa nasa tarihin ne a matsayin ɗan wasa ɗaya tilo da ya riƙe wannan ƙadamin da kulob uku na Ingila kaɗai da suka haɗa da Leicester City, Everton da kuma Tottenham Hotspur.

Kamar yadda shafin Wikipedia ya rawaito Lineker ya ci ƙwallaye 95 a Leicester City ciki wasa 194, ya ci ƙwallaye 30 a Everton cikin wasa 41, ya ci ƙwallaye 42 a Barcelona cikin wasa 103, 67 cikin wasa 105 a Tottenham Hotspor, ƙwallaye 4 a wasa 18 a kulab ɗin Nagoya Grampus da ya yi ritaya.

Sannan ya ci wa ƙasarsa ta Ingila ƙwallaye 48 cikin wasa 60.

Bayan ya yi ritaya, gwarzon ya karɓa wa Ingila kyaututtuka 80 har ya rikiɗe zuwa aikin jarida.

Ya fara aiki da BBC inda ya shafe lokaci mafi tsawo a tarihi a matsayin mai gabatar da shirin Match of The Day.

Daga bisani ya yi aiki da wasu kafafen yaɗa labarai da suka haɗa da Al Jazeera Sports, Eredivisie Live, NBC Sports Network, da BT Sport’s.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *