January 24, 2025

‘Ba za mu iya biyan albashin da ‘yan kwadago ke nema ba’

3
WhatsApp-Image-2024-05-13-at-12.41.10-PM-1024x682.jpeg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iya biyan naira 494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba, kamar yadda ƙungiyar ƙwadagon ƙasa ta buƙata.

Mohammed Idris ya ce biyan buƙatar ƴan ƙwadagon na nufin gwamnati za ta kashe naira tiriliyan tara da rabi wajen biyan albashin ma’aikata, lamarin da ya ce zai jefa walwalar ƴan Najeriya fiye da miliyan 200 cikin barazana.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja babban birnin Najeriya, ministan ya ce gwamnatin tarayya ta amince da biyan naira dubu 60 a matsayin mafi ƙarancin albashi, wanda ke nufin ƙarin kashi 100 ke nan na ƙarancin albashin, kuma tuni kamfanoni masu zaman kansu suka amince da hakan.

Ministan yaɗa labaran ya buƙaci ƴan ƙwadagon su koma teburin tattaunawa da gwamnati domin samar da mafita a kan lamarin.

3 thoughts on “‘Ba za mu iya biyan albashin da ‘yan kwadago ke nema ba’

  1. An excellent read that will keep readers – particularly me – coming back for more! Also, I’d genuinely appreciate if you check my website QN5 about Blogging. Thank you and best of luck!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *