Ba mu yarda da albashin naira 48,000 ga ma’aikatan Najeriya ba—Ƴan ƙwadago
Daga Sodiqat Aisha Umar
Ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun yi watsi da tayin da gwamnatin tarayya ta yi na naira 48,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙaranci ga ma’aikatan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC suka fitar, sun bayyana tayin na gwamnatin tarayya a matsayin abin ban takaici.
A kan haka ne ƙungiyoyin ƙwadagon suka yanke shawarar ficewa daga tattaunawar da ake yi kan mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata, tare da yin kira ga gwamnati da ta sake tunani domin gabatar da tayin da ya fi dacewa domin samun matsayin.
A bayan ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta gabatar da buƙatar tsayar da mafi ƙarancin albashi a kan naira 615,000.
NLC ta ce ta yi hakan ne la’akari da halin matsin rayuwa da tashin farashin kayan masarufi da al’ummar ƙasar ke fuskanta.
Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi ne tun bayan da shugaban ƙasar ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
But I also hope that we learn something about the people who do this work.How close are we? When reading about an anticipated technological advance,リアル エロ