‘Ba mu ji daɗin kisan matashi da sojanmu ya yi ba a Zaria’
Daga: Abdullahi I. Adam
A wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta fitar yau Laraba, rundunar ta yi da-na-sani kan yadda wani sojanta ya kashe wani daga cikin masu zanga-zanga a Samaru da ke Zaria a jihar Kaduna.
A sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce rundunar ta samu kiran neman agaji ne cewa a jiyan an sami wasu ɓata-gari sun yi gangami a Samaru suna ƙona tayoyi a titi tare da neman tada husuma a garin.
Bayan samun kiran ne sai jami’an tsaro su ka je Samarun domin su tarwatsa su ganin cewa gwamnatin ta Kaduna ta saka dokar hana fita a Zaria.
Bayan isan dakarun sojin ne, inji sanarwar, sai wasu daga cikin masu zanga-zangar ya fara kai wa sojojin farmaki wanda hakan ne ya sa wani soja ya yi harbi na gargaɗi, sai dai cikin rashin sa’a harsashi ya samu wani yaro mai shekara 16 mai suna Isma’il Mohammed.
Rundunar sojin ta ce a yanzu haka ana bincike kan wannan sojan da ya yi harbin bayan an tsare shi tun bayan faruwar lamarin.
Tun a jiyan ne dai aka tura wata tawaga ta musamman domin zuwa ta yi ta’aziyya ga iyalan matashin, kamar yadda shugaban rundunar sojin ta ƙasa ta Najeriyar, Laftna Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ya sanar.
Bayanai da TCR Hausa ta samu sun tabbatar da cewa wasu wakilai daga dakarun rundunar sojin ma sun halarci jana’izar matsayin wadda aka gudanar a Samarun.