Ba kuɗi ko shaharar Mane ba ne suka sa na aure shi—Aisha Tamba
Daga Sabiu Abdullahi
Matar Sadio Mane, Aisha Tamba, ta nuna cewa ba kudi ko shahara ba ne suka sa ta aure shi.
A cewarta, shahara da kudin Mane ba za su canza ta ba.
Ta bayyana cewa a shirye take ta fuskanci kalubalen da ke tafe a rayuwar aurenta.
Idan mai karatu zai iya tunawa, Mane ya auri Tamba ne a wani biki na sirri a Dakar, Senegal, a makon jiya.
Da take magana game da rayuwar aurenta, Tamba ta ce, “Ina farin ciki da sabuwar rayuwata kuma na san cewa za ta bambanta sosai. Amma ba na jin wani matsin lamba saboda shaharar Sadio da kuɗinsa ba za su canza ni ba. Wannan ba shi ne abin da nake sha’awa ba.
“Zan kasance mai tawali’u mai himma ga bangaskiyata.
“Amma ina matukar alfahari da zama Madam Mane.”




масло тайф http://e-taif.ru .