Ba dalilin siyasa ba ne ya sa muka kama mai Telegram—Macron
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karyata rade-radin da ake yi na cewa kamen da aka yi wa mutumin da ya kafa Telegram Pavel Durov na da alaka da siyasa, yana mai cewa hakan ya faru ne sakamakon wani bincike na shari’a.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Macron ya jaddada ‘yancin bangaren shari’a na Faransa da kuma rashin tsoma bakin gwamnati a cikin shari’a.
Kalaman na Macron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce dangane da kamun da aka yi wa Durov, inda wasu ke nuna cewa akwai hannu da aka sa a siyasance.
Duk da haka, shugaban ya tabbatar da cewa an ba da damar tsarin shari’a ya gudanar da aikinsa, wanda ya kai ga tsare Durov.
“Na ga bayanan karya game da Faransa bayan kama Pavel Durov,” Macron ya rubuta. “Faransa na da matukar himma ga ‘yancin fadin albarkacin baki da sadarwa, da kirkire-kirkire, da kuma ruhin kasuwanci. Zai kasance haka.”
Shugaban ya bayyana rawar da bangaren shari’a ke takawa wajen tabbatar da dokar, yana mai cewa, “Ya rage ga bangaren shari’a, cikin cikakken ‘yanci, su tabbatar da doka. An kama shugaban kamfanin Telegram a kasar Faransa ne a wani bangare na shari’a da ake ci gaba da gudanarwa.”