Ba a biyan harajin da za a iya yin muhimman ayyuka a Najeriya—Bill Gates

Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, Bill Gates, ya bayyana cewa harajin da ake tarawa a Najeriya ya yi kadan, wanda hakan ke zama kalubale ga samar da isassun kudade ga bangarori masu muhimmanci kamar kiwon lafiya da ilimi.
Da yake magana a wani taron tattaunawa na matasan Afirka kan abinci mai gina jiki a Abuja, Gates ya ce, “A tsawon lokaci, akwai tsare-tsare da Najeriya za ta baiwa gwamnati kudade fiye da yadda take yi a yau. Haqiqa harajin da ake tarawa a Nijeriya ya yi karanci.”
Gates ya sake nanata bukatar gudanar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya don samun amincewar ‘yan kasar kan iyawar gwamnati na samar da ingantaccen kiwon lafiya.
Ya ce, “Idan ‘yan kasa suna son ilimi da kuma abubuwan kiwon lafiya, yayin da suke da tabbacin cewa za a iya gudanar da wadannan shirye-shirye sosai… gudanar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya na matakin farko … ‘yan kasa za su kawo kiwon lafiya a matakin farko, wanda na daga cikin abubuwan da ya kamata a ba da su sosai yayin.”
Kalaman Gates na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji ya gabatar da dokar kara harajin karin VAT daga kashi 7.5% zuwa kashi 10%.
Shugaban kwamitin Taiwo Oyedele ya ce, “Muna da muhimman batutuwa a cikin kudaden harajin da muke samu. Kudaden shiga na kasar nan ya yi kadan. Dokar da muke gabatarwa majalisar dokokin kasar ta nuna cewa kashi 7.5% z koma kashi 10% daga shekarar 2025.”