January 14, 2025

Baƙuwar cuta ta ɓulla a Zamfara

0
IMG-20240512-WA0017.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

An sami ɓullar wata baƙuwar cuta a jihar Zamfara wadda har yanzu likitoci sun kasa gano kanta.

Bayanai na farko-farko da muka samu sun tabbatar da cewa cutar na da bantsoro da saurin rikita jikin waɗanda suka kamu da ita ba tare da ɓata lokaci ba.

Kamar yadda bayanai suka nuna, cikin wanda ya kamu da cutar kan kumbura kuma har ta yi kisan mutane huɗu bayan ɓullarta inda kuma wajen mutum 177 ke kan jinya kamar yadda kafar sadarwa ta BBC Hausa ta rawaito.

Mal. Sulaiman Bala Idris, wanda shi ne mai magana da yawun gwamnan jihar, ya shaida wa BBC cewa, “yanzu gwamnati na son a fahimci cewa wacce irin cuta ce? da kuma fara killace waɗanda suka kamu da cutar saboda gudun yaɗuwarta.”

A zantawar TCR Hausa da Comrade Nura Bello Darajakaset Gusau, wanda mai bibiyar lamura ne a jihar, ya bayyana cewa cutar a yanzu haka ta bayyana ne a ƙananun hukumomin Shinkafa da kuma Maradun, sannan ya yaba da irin matakan gaggawa da gwamnati ke ɗauka wanda a yanzu haka suna aiki tuƙuru kan shawo kan cutar.

Har yanzu ba’a samar ma cutar da wani suna ba kasancewarta baƙuwa ce kuma tana da yanayi mai ruɗarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *