Auren Sadiya Haruna da G-Fresh ya ƙare
Daga Salman Isah
Bayan tsawon lokaci da suka shafe suna ɗauki ba daɗi kan batun rabuwar aure a tsakaninsu, Sadiya Haruna ta ce ta yada ƙwallon mangwaro ta huta da ƙuda.
Ta shaida wa gidan rediyon Freedom da ke Kano cewa ta biya G-Fresh Naira 500,000, kuma ya ba ta takardarta.
Amma duk wani yunƙuri ta jin ta bakin G-fresh kan wannan lamari ya ci tura.