January 14, 2025

Aure: Gwamnatin Kano ta soke lefe

1
image_editor_output_image-901647336-1705674071175.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Mahawara ta kaure a kafefen sada zumunta na zamani kan wata dokar aure da Jihar Kanon ta kafa kan dakatar da lefe da wasu lamura da suka jiɓanci aure da wasu bukukuwa a faɗin Jihar.



A ta bakin Kwamishinan Sharia na jihar, lefe da dangoginsa haramttattun abubuwa ne a dokokin Jihar Kano, duk ya bayyana cewa saɓanin yadda jama’a da dama ke tunani, dokar tsohuwar doka ce kuma a iya saninsa ba a sami wani ƙorafi kan dokar ba ko wani neman sauya ma dokar fasali.

Kamar yadda Kwamishinan ya tabbatar, ya ce dokar an yi ta ne ta a shekarar 1988, wato yau kimanin shekaru 36 kenan.

Kamar yadda bayanai Suka nuna, wani matshin lauya ɗan asalin Kanon, Bar. Abba Hikima ne ya soma takalo tattaunawar inda ya wallafa shafin kundin dokar ta shekarar 1988 wadda bayan haramta lefen, dokar ta soke zaman ajo, garar haihuwa d zaman yin biki.

Banda wannan ita dai dokar ta ayyana kuɗin ‘yan mata da wasu abubuwa da dama a matsayin ababen da gwamnatin ta Kano ba ta amince da su ba yayin gudanar da bukukuwa.

Muhawarar da ake ta tafkawa kan lamarin ba ta rasa nasaba da halin da matasa da dama ke ciki na fama da rashin abin hannu, wanda hakan ya tilasta ma da yawa daga cikinsu jinkirta aure saboda ɗawainiyoyi da auren ke tattare da su.

Da suke bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin, matasan sun ta kawo irin matakan da za su ɗauka in dokar ta fara aiki ka’in da na’in.

Wata matshiya mai suna Ummeey Moh’d Hudu ta ce matuƙar ba a mata lefe ba, to lallai ita ma ba za a yo mata kayan ɗaki ba.

Wani matashi mai suna Nasiru Abubakar ya ce tabbas soke lefe rahama ne ga maza.

Har yanzu dai ana kan tafka zazzafar muhawara mai jan hankali tsakanin matasa.

1 thought on “Aure: Gwamnatin Kano ta soke lefe

  1. wonderful submit, vsry informative. I wonder whyy thhe othher expetts of tyis sector doo nnot
    notice this. You hould continue yoour writing. I’m confident, you have a hugve readers’ base already!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *