Atiku Ya Soki EFCC Kan Kama Gudaji Kazaure

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) kan kama da kuma tsare tsohon ɗan majalisar wakilai na tarayya, Hon. Muhammad Gudaji Kazaure.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana cewa wannan mataki da EFCC ta ɗauka ya saɓa wa doka.
“EFCC ta sake aikata abin da ta saba na take doka, ta hanyar kamawa da kuma tsare ƴan ƙasa da ba su aikata laifin komai ba,” in ji shi.
Atiku ya tuna da yadda hukumar ta kama fitaccen ɗan gwagwarmaya, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da Verydarkman, amma daga bisani ta sake shi sakamakon matsin lamba daga jama’a.
“Yanzu kuma hukumar ta koma kan Gudaji Kazaure. Sun kama shi ba tare da yin wani bayani na laifi da suke tuhumarsa da aikatawa ba.
“An ɗauke shi daga Kano zuwa Abuja, kuma har yanzu babu wani bayani da EFCC ta yi wa iyalansa da kuma ƴan Najeriya,” in ji Atiku.
Ya ƙara da cewa, ko da mutum yana da laifi, kamata ya yi a tunkare shi ta hanyar da doka ta tanada.
“Hakkin hukumar ne ta fito ta yi wa jama’a bayani kan abin da ya sa ta kama Kazaure, kuma bai kamata su riƙa tsare mutane da sunan yin bincike ba.
“Ƴan Najeriya sun zuba ido suna kallo. Kuma tarihi ba zai manta ba,” a cewar Wazirin Adamawa