December 7, 2025

Atiku Ya Jajanta Kan Rasuwar Sheikh Idris Abdulaziz

images - 2025-04-04T122910.458

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya aike da saƙon ta’aziyya bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya bayyana marigayin a matsayin malami mai jajircewa wajen kira da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

“Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi fitaccen malami ne da ke kira da zaman lafiya a tsakanin Musulmi. A ƙarshe-ƙarshen kalamansa a filin Idi a Bauchi, ya sake nanata bukatar zaman lafiya tsakanin al’umma,” in ji Atiku.

Ya ƙara da cewa ilimi da hikimar marigayin sun taimaka matuƙa wajen ciyar da al’umma gaba, yana mai bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya, ba iyalansa kaɗai ba.

“Ina addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya saka masa da aljanna, Ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi,” in ji Atiku.