May 17, 2025

ATBU Ta Kori Laccaranta Bisa Zargin Neman Lalata Da Wata Ɗaliba Matar Aure

images - 2025-04-24T142023.065

Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ya kori wani babban malami, Dr Usman Aliyu, bisa zargin da ake masa na cin zarafin wata daliba mai aure, wato Mrs Kamila Aliyu, wacce ke karatun digiri na biyu a jami’ar.

Wannan hukunci ya fito ne daga rahoton cikin gida na jami’ar da aka wallafa a ATBU Herald (Vol. 39 No. 5, 22 ga Afrilu), bayan zaman taron kwamitin gudanarwa na 96 da aka yi a ranar 11 ga Afrilu, 2025.

A cewar rahoton da manema labarai suka samo, kwamitin ya amince da hukuncin korar Dr Aliyu ne bayan binciken da Kwamitin Ladabtar da Ma’aikatan Manyan Ma’aikata ya gudanar, wanda ya tabbatar da cewa malamin ya aikata laifi.

A bara ne Mrs Aliyu ta rubuta koke zuwa jami’ar, inda ta zargi Dr Aliyu da cin zarafi da kuma barazanar hana ta ci gaba da karatu idan ta ki amincewa da bukatunsa.

Sai dai duk da cewa Dr Aliyu ya maka dalibar, da sashe da jami’ar ƙara a kotu bisa zargin bata masa suna, hakan bai hana jami’ar ci gaba da gudanar da binciken cikin gida ba.

A cewar wata sanarwa daga Babban Mataimakin Rajistara, Alhaji Abdullahi Suleiman, matakin korar ya dogara ne da tanadi na “Babi na 3, Sashe na F, sakin layi na I (o)” na kundin dokokin aikin manyan ma’aikatan jami’ar.

Takardar korar ta kuma umurci Dr Aliyu da ya mayar da dukkan kadarorin jami’ar da ke hannunsa.