January 15, 2025

Arewa: Me ya sa ƴan Kudu suka fi mu cigaba?, daga Adamu Bello Karofi

0
FB_IMG_1718168662650.jpg

Daga Adamu Bello Karofi

Daya daga cikin dalilan dayasa ‘yan kudu suka fimu cigaba shi ne rashin ko in kula da harqar boko damuke dashi. Duk da mun fi su damar samun karatun cikin sauqi.

A lokacin da muka rubuta jarabawar zamantowa cikakken ‘pharmacist’ wanda ake kira da ‘PEP’, a Nigeria mutane dubu daya da dari daya da sittin da uku ne(1,163) muka rubuta jarrabawar.

Amma kwata-kwata ‘yan Arewa Hausawa mu dari da arba’in ne(140) ne. Sauran duk ‘yan kudu da wanda ba Hausawa ba. Mun yi bincike a kwanakin baya a kan yawan kamfanonin hada magani da muke da su a Arewa. 

Sai muka gane duk Arewa maso Gabas wato (North East) babu kamfanin magani ko da kwalli daya. Haka kuma duk Arewa maso yamma kamfanonin basu wuce bakwai(7) ba.

Bayan kuma Kudu Maso Yamma (South West) suna da kusan guda dari(100) su kuma Kudu Maso Gabas (South East) suna da wurin guda hamsin(50).

Wannan kadan kenan daga cikin yanda aka barmu a baya. ‘Yan uwan mu da suke ganin be kamata a bada muhimmanci wa karatu me zurfi ba ko kuma kowa yakoma kasuwanci wannan kuskure ne babba.

Matsalar mu a yau bawai yawan masu karatu bane. Domin bamu da masu karatun ma dayawa. Matsalar mu rashin masu karatu me inganci ne. Kowa yana karatu ne don yasamu kudi wanda hakan be kamata ba.

Muna buqatar masu karatu da gasken gaske don su kadai ne zasu iya nema mana mafita daga qangin talauci da rashin aikin da muka samu kan mu aciki. Bill Gates be gama jami’a ba.

Amma kullum idan yasamu dandazon matasa kiran su yake dasu je jami’a su sami degree. Elon Musk yace ‘graduates’ masu tsantsan kwakwalwa kawai yake dauka a kamfanonin sa. Haka Jeff Bezos.

Idan kowa yace ze koma sayar da kayan gwari a Arewa ina zamu samu wanda zasuyi bincike su fito mana da hanyoyin da zamu na sarrafa wadannan kayayyakin ba tare da sun lalace ba?

Idan kowa yace ze koma gyaran mota ina zamu samu wanda zasu yi bincike su fito mana da yanda zamu qirqiri motocin da suka dace da yanayin mu?

Wadannan abubuwa ne da ba’a iya yin su a fagen kasuwa se de a dakin bincike. Don haka muna buqatar ‘researchers’, ‘scientists’, ‘physicists’, ‘Economists’, ‘Surgeons’, ‘Engineers’ da sauran masu zurfin karatu. Allah yasa mudace!!!

Adamu Bello Karofi ƙwararre ne a fannin haɗa magungunan Bature.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *