January 15, 2025

Arangama Tsakanin Sojoji Da Ƴan Bindiga A Mangun Jihar Filato Ya Sanadin Mutuwar Mutum 30

0
images-2024-01-27T200918.721.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni sun ce an kashe mutane da dama yayin da sojoji da ‘yan bindiga suka yi arangama a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, a safiyar ranar Asabar.

Rikicin ya faru ne bayan Gwamna Caleb Mutfwang ya sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka kafa a yankin.

Mutfwang ya ce bayan inganta tsaro, ya kamata a sanya dokar hana fita daga karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe ‘yan bindiga kusan 30 yayin da wasu sojoji suka samu raunuka a rikicin da aka yi a kauyukan Satguru da Tyop.

Wani jami’in tsaro da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa, “Lamarin ya faru ne tsakanin karfe 7 zuwa 7:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka zo da yawansu, suka fara kai farmaki kan wasu mutane da ke kan hanyar Gindri. Ba tare da bata lokaci ba aka sanar da sojoji kuma nan take suka kawo ɗauki.

“An kashe kusan 30 daga cikin ‘yan bindigar yayin da sama da 50 daga cikinsu aka kama da bindigogi da harsasai. Haka kuma sojoji hudu sun samu raunuka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *