APC ta dakatar da shugabanta na ƙasa bisa zargin cin hanci da rashawa
Daga Sabiu Abdullahi
An dakatar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa, daga shiyyarsa ta jihar Kano bisa zargin cin hanci da rashawa.
Jami’an zartarwa na gundumar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin-Tofa a jihar Kano ne suka bayyana hakan a ranar Litinin.
Haladu Gwanjo, mashawarcin bangaren shari’a na Unguwar, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a babban birnin jihar, ya ce ana zargin tsohon Gwamnan Kano da aikata muguwar dabi’a da almubazzaranci da dukiyar al’umma a lokacin gwamnatinsa a Kano.
Gwanjo ya ci gaba da bayyana cewa, dakatarwar da aka yi wa Gandujen ta biyo bayan kada kuri’ar rashin amincewa da shi ne.
An yanke wannan hukuncin ne saboda gazawarsa wajen wanke kansa daga zarge-zargen cin hanci da rashawa, musamman faifan bidiyon da ake yadawa da ke nuna yana karbar daloli a matsayin cin hanci daga wani dan kwangila.
Dakatar da Ganduje, wanda fitaccen jigo ne a cikin jam’iyyar APC, ya nuna aniyar jam’iyyar na magance zarge-zargen cin hanci da rashawa.





Geothermal HDPE Pipes in Iraq Elite Pipe Factory in Iraq is at the forefront of providing advanced geothermal HDPE pipes, designed specifically for efficient and sustainable geothermal energy systems. Our geothermal HDPE pipes are crafted to offer excellent heat resistance, flexibility, and longevity, making them perfect for ground-source heat pump systems and other geothermal applications. With a commitment to quality and innovation, Elite Pipe Factory stands out as one of the leading and most reliable manufacturers in Iraq. We ensure that our geothermal HDPE pipes meet the highest industry standards, offering superior performance and durability. Discover more about our geothermal solutions by visiting elitepipeiraq.com.