Ancelotti Ya Bayyana Abin da Bellingham Ya Fada wa Lafari Kafin Ya Ba Shi Jan Kati a Wasan Osasuna

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya bayyana abin da Jude Bellingham ya fada wa alkalin wasa Munuera Montero kafin a kore shi a wasan da suka tashi 1-1 da Osasuna.
A wasan da aka buga a ranar Asabar, Kylian Mbappe ne ya fara zura kwallo a ragar Osasuna tun farkon wasa a gasar ta LaLiga.
Sai dai alkalin wasa Montero ya ki bayar da hukuncin fanareti a wasu lokuta uku da Real Madrid ke ganin sun cancanci samu, lamarin da ya harzuka Bellingham.
A lokacin da ake shirin doke kwallo daga baya a minti na 39, Bellingham ya bayyana takaicinsa ga alkalin wasa, wanda hakan ya sa aka ba shi jan kati kai tsaye saboda nuna rashin da’a.
Da yake magana bayan wasan da aka buga a filin El Sadar, Ancelotti ya ce:
“Ina ganin alkalin wasa bai fahimci Turancin Jude Bellingham ba.
“Ya ce ‘f*** off’ ba ‘f*** you’ ba… kuma akwai banbanci mai girma a tsakaninsu.
“Ba zan yi magana da yawa kan alkalin wasa ba, domin ina so in zauna a benci a wasan mako mai zuwa.”
Shi ma Bellingham ya bayyana cewa akwai kuskuren fahimta tsakanin su da alkalin wasa.
Ya ce: “Ba ni da wata mummunar niyya ga alkalin wasa. A bayyane yake cewa kuskuren sadarwa ne.
“Maganar da na fada kamar yadda ‘yan Spain ke cewa ‘j***r’ ce… amma hakan ya sa muka ragu da ‘yan wasa goma.
“Ba zagi ba ne, wata magana ce kawai da na fada wa kaina.”