January 14, 2025

Ana zargin sojojin Isra’ila da kama ɗaruruwan Falasɗinawa tare da barinsu cikin yunwa da ƙishirwa

0
image_editor_output_image-2063852777-1702883654488.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Sojojin Isra’ila sun kakkama daruruwan Falasdinawa a yankin arewacin Zirin Gaza, inda suka raba su da iyalansu tare da tilasta wa maza tube riga kafin su tasa ƙeyarsu zuwa magarkama da ke gabar teku.

A cewar wani rahoto na AP, Falasdinawan da aka kama sun shafe sa’o’i cikin fama da yunwa da sanyi kamar yadda masu rajin kare hakkin bil’adama da ‘yan uwansu da kuma fursunonin da aka sake suka bayyana.

Falasdinawa da ake tsare da su a garin Beit Lahiya da sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya da kuma unguwannin birnin Gaza sun ce an daure su, tare da rufe musu idanuwa.

Wannan na zuwa ana a daidai lokacin da al’amurra suke kara tsamari da ta’azzara a yaƙin da ake yi tsakanin Hamas da Isra’ila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *