Ana zargin Emefiele da buɗe asusun banki sama da 500 a sassan duniya ba bisa ka’ida ba
Daga Sabiu Abdullahi
Ana zargin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da cewa ya ajiye biliyoyin naira ba bisa ka’ida ba a cikin asusun banki 593 a Amurka, Burtaniya, da China
A cewar rahotanni, Emefiele ya mallaki waɗannan asusun ne ba tare da amincewar da ake bukata daga kwamitin gudanarwa zuba jari na babban bankin ba.
Mai bincike na musamman kan CBN da abubuwan da ke da alaƙa, Jim Obaze, ya gano cewa Emefiele ya ba da fam 543,482,213 a cikin asusun ajiya a bankunan Burtaniya kaɗai ba tare da wani sahihin izini ba.
Duk da yunƙurin isa ga lauyan Emefiele, Mathew Bukkaa don Jin ta bakinsa game da lamarin, babu wata amsa da aka samu a lokacin gabatar da wannan rahoton.