January 13, 2025

An yi wa sojoji sama da 100 ƙarin girma

1
Taoreed-Lagbaja.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Majalisar Sojan Najeriya ta kara wa jimillar Birgediya Janar 47 girma zuwa matsayin Manjo Janar.

Sannan ta ƙara wa kanar-kanar 75 zuwa matsayin Birgediya Janar.

Wannan cigaban nasu na zuwa ne bayan ritayar janar 113 a ranar Laraba.

Sai dai wata sanarwa a ranar Juma’a da Daraktan Hulda da Jama’a na Sojoji, Brig. Janar Onyema Nwachukwu, ta ce majalisar ta amince da karin girma da manyan jami’an suka yi a ranar Alhamis.

Janar Onyema ya kuma nuna cewa babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya bukace su da su rubanya kokarinsu na tabbatar da daukakarsu da kuma kwarin gwiwar da ake da ita a kansu

1 thought on “An yi wa sojoji sama da 100 ƙarin girma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *