March 28, 2025

An yi jana’izar Sarkin Gobir yayin da har yanzu gawarsa take hannun ƴanbindiga

IMG-20240821-WA0026

Daga Sabiu Abdullahi   

An yi jana’izar Alhaji Isa Muhammad Bawa, Sarkin Gobir na gundumar Gatawa a Jihar Sakkwato, ba tare da gawarsa ba, bayan da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da shi, da azabtarwa da kuma kashe shi a ranar Laraba.   

A cewar wani ma’abocin dandalin sada zumunta na Facebook, Sarkin Yaqi, an gudanar da jana’izar ne bisa ka’idar addinin Musulunci, wanda ya ba da damar yi masa Sallah ba tare da gawarsa ba.   

“An kammala jana’izar Sarkin Kudun Gobir, an yi jana’izar ba tare da gawa ba kamar yadda addinin Musulunci ya ce idan haka ta faru,” inji Sarkin Yaki.   

‘Yan ta’addan da suka kashe Alhaji Bawa sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 60 da babura biyar domin a sako gawarsa domin a binne shi yadda ya kamata.   

An sace Alhaji Bawa ne tare da dansa a watan Yuli kuma wani faifan bidiyo mai cike da damuwa ya bayyana wanda ke nuna shi yana rokon a ceto shi tare da rokon gwamnati ta sa baki.

Duk da rokon da ya yi, ‘yan ta’addan sun kashe shi a ranar Laraba.   Tun da farko dai masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su makudan kudade har Naira biliyan daya domin a sako su.