November 5, 2024

An yi jana’izar mutane 14 cikin 18 da suka rasu a wajen rabon Zakka a AYM Shafa a Jihar Bauchi

0


Daga Muazu Haɗawa

Na je mƙabartar Bauchi Dungulbe a yammacin Lahadi 24/3/2024 inda aka yi jana’izar mutane 14  duk mata wanda suka rasu a wajen turereniyar karɓar zakka a ofishin AYM Shafa da ke Bauchi.

Waɗanda aka yi jana’izarsu su ne kamar haka:

1. Alti Abdullahi Digan mai shekaru 55.
2. Maryam Sulaiman Kandahar mai shekaru 18 3. Nana Khadija Sulaiman Kobi mai shekaru 7
4. Aisha Ibrahim Kobi Mamar Khadija.
5. Maryam Shayibu Gwabba mai shekaru 16.
6. Aishatu Usman Gwangwangwan mai shekaru 13.
7. Hauwa Musa Sabon Kaura mai shekaru 50.  8. Aishatu Saidu Kandahar mai shekaru 55.
9. Amina Abdullahi Kandahar mai shekaru 40.
10. Umaima Yahaya Unguwar Isa Ali mai shekaru 13.
11. Sahura Abubakar Unguwar Bauchi mai shekaru 48.
12. Zainab Ahmad Zango mai shekaru 8.
13. Khadija Yahaya Madina Qtrs mai shekaru 5.

Labarin da na samu daga Asibitin TH akwai mutane 9 a ’emergency’ an shigar da kusan mutane goma cikin asibiti kuma an sallami mutane sama da 40 da suka ji rauni.

Sauran mutane da suka rasu kuma bamu sani ba ko sai gobe a kawo su ko luma an kai su wata maƙabarta ko wani garin.

Daga Muazu Hardawa Editan Jaridar Alheri Dandalkura Radio Reporter Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *