An Yi Jana’izar Ma’aikatan Matatar Ruwan Gubi Dam a Bauchi

Daga Sabiu Abdullahi
An gudanar da sallar jana’iza ga ma’aikata hudu da suka rasa rayukansu a yayin da suke gudanar da aikin tsaftace matatar ruwan Gubi Dam da ke cikin garin Bauchi, jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan sun nutse ne a cikin matatar ruwan yayin da suke aiki, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin da ma jihar baki ɗaya.
Wadanda suka rasu su ne:
Ibrahim Musa
Shu’aibu Hamza
Jamilu Yunusa
Abdulmalik Ibrahim Hamza
An gudanar da sallar jana’izar marigayan a cikin garin Bauchi, inda daruruwan mutane suka halarta domin yi musu addu’a tare da jajanta wa iyalansu da abokan arziki.
Al’umma da dama sun bayyana alhinin su tare da roƙon Allah ya jikansu da rahama, ya gafarta musu kurakuransu, kuma ya ba iyalan su hakuri da juriya.