January 13, 2025

An yi hasashen farashin kayan abinci zai ƙara tashin gwauron zabi a 2024

0
images-2024-01-05T081335.731.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni da suke shigowa na nuna cewa za a samu tashin farashin kayan abinci a ƙasashen Afirka, musamman Najeriya.

Daga cikin kayan abincin da aka ambato za a samu tashin farashin a kansu sun haɗa da gero, dawa, masara, shinkafa, alkalama da sauran kayayyakin masarufi.

A cewar wani rahoton da BBC Hausa ta fitar yau da safe, wannan labari “yana kunshe ne cikin wani rahoto mai taken ‘Kasuwancin Yankin Yammacin Afirka’ da hukumar abinci da aikin gona ta duniya FAO ta fitar.”

BBC ta ƙara da cewa, “Rahoton ya danganta lamarin da wasu abubuwa da suka hada da raguwar samar da kayayyaki, da takunkumin kasuwanci, da rashin tsaro da karyewar darajar kudaden kasashen.

“Ya kuma yi gargadin cewa wannan na iya haifar da ƙalubale ga samun abinci da wadata shi a yankin, abun da ke bukatar daukar matakin gaggawa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *