January 14, 2025

An yanke wa tsohon dan wasan Barcelona Dani Alves hukuncin zaman gidan yari bisa laifin cin zarafi

0
images-194.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

An yanke wa tsohon dan wasan Barcelona da Brazil Dani Alves hukuncin daurin shekaru hudu da watanni shida a gidan yari saboda zargin laifin yin lalata da wata.

Kotu ta yanke hukuncin, wanda ya haifar da martani nan take daga ɓangaren lauyoyin Alves.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, lauyan Alves, Inés Guardiola, ya bayyana aniyarsu ta daukaka kara kan hukuncin, tare da tabbatar da cewa Alves ba shi da laifi.

Guardiola ya bayyana kwarin gwiwa na soke hukuncin, tare da bayyana imaninsa ga rashin laifi Alves duk da hukuncin da kotun ta yanke.

Bugu da ƙari, an umarce shi da ya biya Yuro 150,000 a matsayin diyya ga wadda abin ya faru da ita, tare da biyan kuɗin shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *