An Yanke Wa Mutum Biyar Hukuncin Kisa Saboda Kashe Tsohuwa Bisa Zargin Maita A Kano

Wata babbar kotu da ke Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutum biyar da aka samu da laifin kashe wata tsohuwa mai shekaru 67 bisa zargin maita.
Kotun ta tabbatar da cewa mutanen sun haddasa mutuwar tsohuwar a ranar 15 ga watan Nuwamba 2023, ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba.
A yayin yanke hukuncin, mai shari’a Usman Na’abba ya bayyana cewa kotu ta samu gamsassun hujjoji da suka tabbatar da laifin waɗanda ake tuhuma.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Daɗin Kowa da ke ƙaramar hukumar Wudil ta jihar Kano.
Batun maita da tsafi na ci gaba da jawo cece-ku-ce a sassa da dama na Afirka, inda wasu iyalai ke ɗaukar doka a hannunsu suna hukunta waɗanda ake zargi da maita, musamman idan ana danganta su da mutuwar yara ko wasu matsaloli.