An yanke wa mutane 5 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe makiyayi a Osun
Daga: Abdullahi I. Adam
Mai shari’a Kudirat Akano da ke babbar kotun jihar Osun ta yanke ma wasu mutane biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin garkuwa da wani makiyayi mai suna Ibrahim Adamu.
Kamar yadda lauyan gwamnati mai shigar da ƙara, Mista Moses Faremi ya bayyana ma kotu yayin yanke hukuncin a jiya Talata, wanda aka hallakan ya rasa ransa ne bayan waɗanda aka yanke ma hukuncin sun yi garkuwa da shi, kuma sun karɓi kuɗin fansa har naira miliyan 3.
Waɗanda su ka aikata laifin su ne Ibrahim Issa, Lateef Bello, Abdul Ramon Soliu, Bello Ibrahim da kuma Abudu Mumini Jolaanobi Saheed, kuma an soma masu wannan shari’a ne tun ranar 28 ga watan Oktoba na shekarar 2021.
Yadda lamarin ya faru, kamar yadda aka bayyana a kotun, shi dai Ibrahim Adamu an zo ne har gidansa da ke Owode-Ede a jihar Osun a ranar 17 ga watan Afrilu na 2018, misalin ƙarfe 7:45 na marece aka yi awon gaba da shi cikin motarsa ƙirar Toyota Corolla, sannan aka tilasta ma iyalansa su biya kuɗin fansa.
Shi dai Ibrahim ya jima yana gudanar da sana’ar shanu a yankin na Owode-Ede, kuma masu garkuwa da shi ɗin sun hallaka shi ne saboda ya gano wani daga cikinsu.
Mai shari’a Kudirat Akano, a yayin yanke hukuncin, ta bayyana cewa waɗanda su ka aikata laifin sun saɓa ma Sashi na 324, da na 319 da kuma na 364 na kundin laifuka na jihar ta Osun.
Waɗanda aka yanke ma hukuncin sun musa tuhumar, sai dai shedu da hujjoji da ɗaya daga cikin ‘yansanda masu gabatar da ƙara, Mista Ganiyu Taofeek ya nuna a kotun waɗanda su ka ƙunshi murya da aka naɗa da kuma takunkumi da su ka yar yayin yunƙurin kame Ibrahim ɗin sun sami amsuwa a kotun.
Sai dai mai kare waɗanda su ka aikata laifin, lauya Bola Ige, ya ce tuhumar da ake ma waɗanda ya ke karewar ba ta da gamsassun hujjoji, wanda hakan ya sa ƙungiyar lauyoyi mai suna “Legal Aid Council” ta nemi kotun da ta tausa a hukuncin.
Daga ƙarshe dai mai shari’a Kudirat Akano ta yanke ma waɗanda su ka aikata laifin hukuncin kisa ta hanyar rataya.