January 15, 2025

An tuɓe dagaci daga sarautarsa a Zazzau

5
IMG-20231107-WA0033.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Rahotanni da suke fitowa jiya Talata sun nuna cewa Majalisar Masarautar Zazzau a bisa jagorancin Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ta warware naɗin Dagacin Awai, Mal. Iliyasu Abdullahi, da ke yankin Maigana ta Ƙaramar Hukumar Soba.

Majalisar ta saurari ƙorafe-ƙorafen jama’a a masarautar tsohon dagacin waɗanda a kansu ne aka dakatar da shi.

A nasa ɓangaren, tsohon dagacin bai musanta zarge-zargen ba, wanda a bisa hakan aka warware naɗin nasa nan take.

Majalisar Masarsutar ta Zazzau ta umurci Hakimin Gundumar Maigana, Dandarman Zazzau Alhaji Lawal Zailani da shirya gudanar da zaɓen sabon dagaci a garin Awai ba tare da ɓata lokaci ba.

5 thoughts on “An tuɓe dagaci daga sarautarsa a Zazzau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *