January 24, 2025

An tsinci gawar wata ɗalibar jami’ar Aliko Dangote

7
IMG-20240503-WA0012.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

An tsinci gawar wata ɗaliba mai suna Aisha Yahaya ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, a wani gida da ke wajen jami’ar.

Aisha, ɗaliba ce da ke matakin karatu na uku wato level 300 a sashen nazarin Kimiyya da Fasahar Abinci na jami’ar wadda aka tsinci gawarta bayan ta koma ɗakinta.

An ce ɗalibar ta rubuta jarrabawarta ta farko a zangon karatun na farko da ake yi a jami’ar.

Wasu daga cikin abokan karatunta sun danganta mutuwarta da shiga cikin matsi da damuwa a dalilin karatu da kuma zana jarrabawar.

A cikin wasiƙar ta’aziyyar, hukumar jami’ar ta bayyana matuƙar baƙin cikinta dangane da rasuwar Aisha Yahaya.

Sanarwar ta ce, “Aisha ɗaliba ce mai hazaƙa wadda ta rasu a dalilin bugun zuciya. Za a riƙa tunawa da ita a kan sha’awarta na karatu da jajircewarta kan harkokin karatunta.”

7 thoughts on “An tsinci gawar wata ɗalibar jami’ar Aliko Dangote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *