January 24, 2025

An tsinci gawar wani mai shiga irin ta mata a Abuja

0
images (7) (13)

Daga Abdullahi I. Adam

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Bennett Igweh, a yau Alhamis, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan mutuwar wani mutumi da har yanzu ba a tantance ba sanye da kayan mata.

Rundunar ‘yan sandan, a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Josephine Adeh, ta fitar ta ce ta samu kiran gaggawa game da gawar wata mata da aka gano a kan hanyar Katampe zuwa Mabushi, inda nan take ta aike da jami’an bincike zuwa wurin.

Adeh ta ce, “A matsayin martani ga kiran da rundunar ‘yan sandan ta samu a ranar 08/08/2024 da misalin karfe 07:40 na safe, an ga wata mace da ba a san ko wace ce ba tana kwance ba ta motsi a kan hanyar Katampe zuwa Mabushi, kuma nan take aka aike da tawagar jami’an tsaro zuwa wurin.

Adeh ta kara da cewa binciken farko da jami’an ‘yan sandan suka gudanar ya nuna cewa mutumin namiji ne sanye da rigar mata ba tare da wata hanyar tantance shi waye ba.

Ta ce nan take aka garzaya da mutumin asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *