May 16, 2025

An Samu Gawar Wani Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya A Otal

images-2025-02-16T132355.305.jpeg

An gano gawar wani sufeton ‘yan sanda mai suna Haruna Mohammed a wani ɗakin otal da ke jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa Mohammed, wanda ke aiki a sashen ‘yan sanda na Ishashi a Legas, ya shiga Super G Royal Hotel da ke Anthony Uzum Estate, Oyeyemi Akute, da wata mace da ba a bayyana sunanta ba misalin ƙarfe 1:00 na safe a ranar Asabar.

Bisa bayanan da aka tattara, manajan otal ɗin, Deborah Adejobi, ta lura cewa ƙofar ɗakin a buɗe take, kuma lokacin da ta duba misalin ƙarfe 8:52 na safe, ta tarar da Mohammed ba shi da rai, yayin da ba a ga macen da suka shigo tare da shi ba.

A cewar wani rahoto na ‘yan sanda, mai otal ɗin, Abiodun Olagunju, ne ya sanar da jami’an tsaro game da lamarin.

“Matar ta sauka a wajen karɓar baƙi misalin ƙarfe 6:00 na safe don neman ruwan sha kafin daga bisani ta yi gaba,” in ji Olagunju.

An kai gawar Mohammed zuwa Life Channel Mortuary da ke yankin Olambe a Akute.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin.

“Da farko, sai da muka samu rigar ‘yan sanda a cikin jakarsa sannan muka fara samun tabbacin cewa ɗan sanda ne. Babu wata katin shaida a tare da shi ko a cikin kayansa,” in ji Odutola.

“Sai daga baya bincike ya tabbatar cewa marigayin sufeto ne a sashen ‘yan sanda na Ishashi da ke Legas. Mun tuntubi DPO, kuma an tantance gawarsa.”

Odutola ta kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun fara neman matar da ta gudu, tare da ci gaba da bincike don gano musabbabin mutuwar sufeton.