An Samu Gagarumin Karin Farashin Mai A Ƙasar Kenya
Daga Mustapha Mukhtar
A Ƙasar Kenya farashin man fetur, kalanzir, iskar gas da disel ne suka yi tashin gauron zabi a rahoton da muka samu yanzu, inda ke nuni da cewa farashin manfetur, iskar gas da disel sun ƙaru. Hukumar kula da ƙayyade farashin makamashin ta ƙasar ce me suna (Epra) ta yi ƙarin yau. An ƙara farashin man fetur ɗin ne da Ksh 5.72 a kowace lita (kwatankwacin ƙarin sama da Naira 25 a kowace lita), disel da 4.48KSH, kalanzir kuma ya samu kari da 2.45KSH.
Wannan gagarumin ƙari ne inda a yanzu ake siyar da fetur a kudi 211.64KSH, a Nairobi, disel 200.99 da kuma kalanzir a farashin 202.61.
Wannan farashin ya samu ne sakamakon tallafin da gwamnati ta zuba na 3.07KSH a kowace litar fetur, 11.64 na disel da kuma 9.6 na kalanzir, wanda jimillar kudin sun kama 1.76billion KSH.
Wannan yana nuni da cewa za a riƙa siyan man fetur ɗin ne a Nairobi babban birnin ƙasar akan farashin KSH217.36 (kwatankwacin sama da Naira 1200 a kowa ce lita).
Idan ba a manta ba a ranar da aka rantsar da shugaban Ƙasar na Kenya me ci Mr. Samuel Ruto, a watan Augusta na shekarar bara, a wannan ranar ya cire tallafin man fetur a ƙasar.
Mr. Ruto ya sanar da sake dawo da tallafin man fetur ɗin a watan Agusta na wannan shekara bayan da rayuwa ta cigaba da tsanani ga mutanen ƙasar ta hanyar hauhawar farashin kayan masarufi.