‘An sace takardun shari’ar cin hanci kan Ganduje a lokacin zanga-zanga’
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bada rahoton cewa masu zanga zanga sun ɗauke duk wasu takardu masu alaka da shari’ar cin hanci da rashawa da aka shigar a gaban shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Ganduje.
Abba Kabir ya jawo hankulan jama’a game da yadda aka zare wannan takarda ta manyan laifukan da ake zargin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje na cin hanci da rashawa daga babbar kotun jihar.
A cikin wata sanarwa ta hannun mai magana da yawunsa, Mista Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya bayyana damuwarsa kan lamarin.
Ya bayyana hakan ne biyo bayan ziyarar gani-da-ido da ya kai kotun a ranar Laraba, inda Gwamna Yusuf ya samu bayani daga babban lauyan gwamnati, babban magatakarda da sauran alkalan babbar kotun.
Gwamnan ya nuna matukar damuwa da bacin ransa kan lamarin, wanda ya haifar da ayar tambaya kan sahihancin tsarin doka a ƙasar.