February 10, 2025

An rantsar da Ramaphosa a matsayin shugaban Afirka ta Kudu karo na biyu

1
Ramaphosa-3.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

An rantsar da Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu a karo na biyu a matsayin shugaban kasa a birnin Pretoria a ranar Laraba.

Babban mai shari’a Raymond Zondo shi ne ya jagoranci bikin rantsar da Ramaphosa a gaban ‘yan majalisa, da manyan mutanen daga kasashen waje. 

An kuma samu halartar shugabannin addini da na gargajiya da kuma magoya bayansa.

Shugabannin kasashe da dama da suka hada da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Joao Lourenco na Angola da Denis Sassou Nguesso na Congo Brazzaville da cikakken shugaban Eswatini Sarki Mswati III sun halarci bikin rantsar da shi.

1 thought on “An rantsar da Ramaphosa a matsayin shugaban Afirka ta Kudu karo na biyu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *