An Raba Yarinya ‘Yar Shekara 2 Da Ranta Sanadiyyar Yi Mata Fyaɗe a Bauchi
Daga Sabiu Abdullahi
A ranar 5 ga Nuwamba, 2024 ne aka kai rahoton wani lamari mai ban tausayi ga hedikwatar ‘yan sanda ta Ningi, wanda ya shafi wata yarinya ‘yar shekara biyu da aka same ta babu rai a gefen wani masallaci a kan titin Deneva a karamar hukumar Ningi.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) SP Ahmed Mohammed Wakil Anipr ya fitar kuma ya sanyawa hannu jiya a Bauchi, yarinyar da aka yi wa fyaden an sami raunuka a jikinta, bayan da aka ci gaba da bincike.
Rahoton likita daga babban asibitin Ningi ne ya tabbatar da munanan raunukan sakamakon shigarta da aka yi, wanda daga karshe ya kai ga mutuwarta.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, CP Auwal Musa Mohammed, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan wannan danyen aikin, inda ya umurci jami’in ‘yan sandan shiyya da ya dauki karin matakai domin kamo wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
A cewar sanarwar, CP Mohammed ya nanata muhimmancin dawainiyar iyaye kuma ya bukaci iyaye da masu kula da su su tabbatar da tsaron ‘ya’yansu tare da hana su yawo su kadai a kan tituna.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi na neman taimakon jama’a wajen bayar da duk wani bayani mai amfani da zai taimaka wajen kamawa da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aikin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Mohammed Wakil, a cikin sanarwa, ya bukaci al’umma da su ba da hadin kai tare da yin taka tsan-tsan.
Ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma an yi kira ga jama’a da su fito da duk wani bayani da zai taimaka wajen kamo su.