An katse intanet a Mauritania bayan zaben shugaban kasa

An katse internet ta wayar hannu tun daren ranar Litinin a babban birnin kasar Mauritania, kamar yadda ‘yan jaridar AFP suka gano, bayan da aka yi taho-mu-gama bayan da aka sanar da cewa Mohammed Ould Cheikh El Ghazouani ne ya lashe zaben shugaban kasa.
Shaidu sun ba da rahoton tashin hankali a gundumomin masu aiki a Nouakchott a yammacin ranar Litinin.
Wannan na zuwa ne sa’o’i bayan sakamakon wucin gadi na karshe ya nuna cewa Ghazouani ya yi nasarar sake lashe zaben a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar.