January 15, 2025

An kashe sojojin Amurka 3 a wani harin jirgi marar matuƙi a Jordan

3
images-2024-01-28T185600.261.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Sojojin Amurka 3 ne suka mutu yayin da 25 suka jikkata sakamakon wani hari da wani jirgin mara matuki da aka kai a sansanin sojin Amurka dake kasar Jordan, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta sanar.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta fitar ta ce an samu hasarar rayukan da aka samu ne sakamakon harin da jirgin sama mara matuki ya kai a wani sansani da ke kusa da kan iyakar Syria.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce “kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi da Iran ke mara wa baya ne suka kai harin”.

Wannan dai shi ne karon farko da aka kashe sojojin Amurka a wani hari da aka kai yankin bayan harin da Hamas ta kai kan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

Fadar White House ta ce an yi wa Mista Biden karin bayani da safiyar Lahadi kan harin.

“Yayin da muke ci gaba da tattara gaskiyar wannan hari, mun san cewa kungiyoyin mayaka masu tsattsauran ra’ayi da Iran ke mara wa baya da ke aiki a Siriya da Iraki ne suka kai shi,” in ji Mista Biden a cikin wata sanarwa.

A halin yanzu dai sojojin Amurka da na kawance suna jibge a tekun Bahar Rum bayan da ‘yan Houthis da ke samun goyon bayan Iran suka fara kai farmaki kan jiragen ruwa na kasuwanci a yankin.

Kungiyar da ke da hedkwata a Yaman ta ce tana kai hare-hare kan jiragen ruwa a yankin ne don nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza, inda Isra’ila ke yaki da Hamas.

Sai dai a baya hukumar tsaron Amurka ta Centcom ta ce wadannan haramtattun ayyuka ba su da alaka da rikicin Gaza.

3 thoughts on “An kashe sojojin Amurka 3 a wani harin jirgi marar matuƙi a Jordan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *