January 15, 2025

An kama wata mata da ake zargin ta kashe mijinta da gatari har lahira a jihar Borno

0
IMG-20240710-WA0020.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A Arewa maso Gabashin Najeriya, za ku ji cewa kama wata mata mai suna Lydia Aji mai shekaru 40 a jihar Borno bisa zargin kashe mijinta da gatari.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yusufu Lawal, ma’auratan sun yi kazamin fada ne a ranar 4 ga watan Yuli, 2024, a gidansu da ke kauyen Kautikari a karamar hukumar Chibok.

Rahotanni sun ce fadan ya samo asali ne a kan ‘yarsu mai suna Rachael ‘yar shekara 13 da ta yi sata tare da sayar da akuya.
Mijin Lydis dai, Aji Makinta, ya bukaci matarsa da diyarsa su bar gidansa bayan faruwar lamarin.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa, “A ranar 4 ga watan Yuli, 2024, wani Bulama Mulikabu ya kawo rahoto a ofishin ‘yan sanda na Chibok cewa, a ranar ne Lydia Aji da mijinta, Aji Makinta, suka yi kazamin fada wanda ya kai ga matar ta kashe mijinta da gatari, inda nan take ya mutu”.

A halin yanzu dai ana gudanar da bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *