An kama wasu suna lalata a cikin coci a Maiduguri
Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kama wani matashi da wata matashiya da laifin yin lalata a cikin Cocin Protestant da ke Kwalejin ‘yan sanda da ke Maiduguri a jihar Borno.
Mutanen da aka kama ɗin dai su ne Kaka Ali Umar wanda ya fito daga titin Damboa da kuma Khadija Adam mazauni unguwar Ngomari a Maiduguri.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
A cewar Rabaran Danjuma Adamu, limamin cocin, an kama mutane biyun ne a cikin harabar cocin.
Rabaran Adamu ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka wulakanta wannan wuri mai tsarki, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya da cin amana.
Rabaran ɗin ya ce, “Mun garzaya cikin cocin, sai ga shi mun gamu da Musulmai biyu da ke wannan aika-aika, inda nan take muka sanar da ‘yan sanda.”
Ya bayyana girman al’amarin, inda ya nuna buƙatar a gaggauta ɗaukar mataki domin kare martabar cocin.
An ce dai mutanen biyu ba su musanta zargin ba, kuma sun yarda sun yin lalata a cikin cocin.