January 14, 2025

An kama wasu mutane 9 da ake zargi da safara da satar yara a Kano

0
FB_IMG_1703827740984.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 9 da ake zargi da aikata laifukan safara da kuma garkuwa da mutane, haɗi da saye da sayar da kananan yara.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel ne ya sanar da kamen a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar rundunar ta Bompai ranar Alhamis.

Gumel ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan wasu jerin hare-hare da jami’an leken asiri suka gudanar, inda suka yi nasarar tarwatsa taron su da suka dade suna yi wanda ya shafi safarar mutane a jihohin Kano, Bauchi, Gombe, Legas, Delta, Anambra, da Imo.

Kwamishinan ya yi karin haske kan kokarin da rundunar ‘yan sanda ta himmatu km a kai wajen ganowa tare da kawar da wadannan muggan laifuka.

An kubutar da mutane bakwai da akasarinsu kanana ne daga hannun wadannan mutane.

Gumel ya bayyana cewa an sayar da yaran da aka ceto masu shekaru tsakanin uku zuwa takwas a kan farashi daga N300,000 zuwa N600,000, gwargwadon shekarunsu.

A yayin bincike, an bayyana cewa an sayar da wani da aka yi garkuwa da shi mai suna Mohammed Ilya, wanda asalinsa aka sace daga Bauchi amma aka canza masa suna zuwa Chidiebere a Nnewi, jihar Anambra.

Kwamishinan ‘yan sandan ya lura da munin lamarin inda ya yi alkawarin hada kai da gwamnatin jihar domin ganin an dawo da duk yaran da aka sace ga iyalansu lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *