May 17, 2025

An kama waɗanda ake zargi da ƙwace bindiga daga hannun ɗan sanda

Recovered-ammunition.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da ake zargi da aikata kashe-kashe a jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce ta kama wasu da ake zargi da kwace bindiga kirar AK 47 daga hannun dan sanda.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Fayoade Adegoke, yayin da yake gabatar da wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka a hedikwatar rundunar da ke Ikeja a ranar Laraba, ya bayyana cewa rundunar ta kuma kwato harsasai da dama daga hannun masu laifin.

Kwamishinan ya ce ‘yan sanda sun kama “Toheeb Oyekunle, Victor Jimoh, Samuel Okanlawon, Segun Babatunde, Pelumi Ajuloye, Mohammed Ibrahim da Bello Ahmed da ke da alaka da harin da aka kai a unguwar Iju Ishaga da ke jihar inda wadanda ake zargin suka kwace bindigar AK47 daga hannun wani jami’in dan sanda.

Wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa a Legas da kewaye.

An kwato AK47 guda daya mai girman gaske.